Super Eagles zasu dafe dala 20,000 kan kowace kwallo a ragar Kamaru
Wani shahararren dan Kasuwa a Najeriya yayiwa tawagar kwallon kafa ta kasar Super Eagles alkawarin cewa zai basu kyautar dala Dubu 20,000, kwatankwacin naira miliyan da dubu dari da saba’in (7,170,000) kan kowace kwallo da su jefa a ragar Kamaru a wasan da zasu fafata yau na neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya ta badi, a birnin Yaounde.
Wallafawa ranar:
Attajirin da ke amsa sunan Udofia, ya sha alwashin yi wa ‘yan wasan na super eagles yayyafin kudin ne sakamakon farin cikin yadda suka lallasa Kamaru da kwallaye 4 – 0 a zagayen farko da suka fafata a garin Uyo.
A halin da ake ciki a yadda jadawalin tsayuwar rukunan kasashen da ke fafata neman cancantar zuwar gasar cin kofin duniyar da za’a yi a Rasha, Najeriya ce kan gaba a rukunin da take ciki na B da maki 9, sai Zambia da maki 4, Kamaru ce ta uku da maki 2 yayinda Algeria ke matsayi na karshe da maki 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu