Isa ga babban shafi
Najeriya

Babbar Kotun Lagos Ta Mallakawa Gwamnati Kudaden da aka tsinta Kusan Naira Miliyan 500

Babbar Kotun Lagos ta bada umarni na karshe na kwace wasu kudaden kasar Naira kusan miliyan 450 da aka samu a wani shago na ‘yan chanji dake Lagos, kasancewar har yanzu babu wanda ya zo karban kudaden.

Shugaban riko na Hukumar EFCC a Najeriya  Ibrahim Magu.
Shugaban riko na Hukumar EFCC a Najeriya Ibrahim Magu. premiumtimesng.com
Talla

Mai sharia Rilwan Aikawa ya bada wannan umarni  bayan ya saurari bayanai daga masu shigar da kara wato Hukumar EFCC.

A cewar Alkalin tunda babu mai su, kudaden sun zama mallakin Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Wata daya kenan  da gano wadannan makudan kudade cikin buhuhuna amma har yanzu babu wanda ya amsa cewa nashi ne duk da cigiya da aka yi ta yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.