Najeriya ta kafa hukumar sa ido kan farashin kayan masarufi
Majalisar zartawar Najeriya ta cimma matsayar kafa wata hukuma ta musamman, da zata sa ido da zata magance hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minsitan yada labaran kasar Lai Mohammed ya sanar da matakin, yayin zantawar da yayi da manema labarai a garin Abuja, jim kadan bayan kamalla taron majalisar, wanda mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Lai Mohammed ya ce ana fatan kafa kwamitin zai kawo karshen yawaitar hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya, wanda hakan ya jefa masu kananan karfi cikin mawuyacin hali a kasar.
Daga cikin wadanda zasu jagoranci hukumar sa idon kan farashin kayan abincin, akwai Ministoci da suka hadar da na sassan albarkatun gona, ma’aikatar kudi, Sufuri, da kuma na albarkatun ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu