Isa ga babban shafi
Najeriya

2face ya bukaci a gudanar da zanga zanga a Najeriya

Fitaccen mawakin Najeriya 2face Idibia ya yi kira ga masoyan shi su fito zanga-zanga a ranar Talatar makon gobe domin adawa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

Mawaki 2face Idibia
Mawaki 2face Idibia
Talla

Zalika mawakin ya bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakan magance matsalar.

2face ya yi kiran ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin shi na facebook, wanda kuma cikin sa’a guda, sama da mutane dubu ashirin da biyu suka kalli sakon.

Kafofin sadarwa na intanet dai sun kasance hanyoyin kiran gangamin zanga-zanga a Afrika, to sai dai kuma abin mamaki ne mawaki ya fito ya dauki irin wannan matsayin na siyasa.

A tataunawarsa da sashin hausa na RFI Saifullahi Ibrahim mawakin Pop da ake kira DR Pure a Kano, ya ce ko da yake, suna goyon bayan kawo karshen matsin tattalin arziki da al’ummar Najeriya ke fuskanta, ba zanga zanga ba ce hanya mafi dacewa wajen jan hankalin gwamnati.

A cewar Dr Pure, kamata yayi mawaka su bi hanyoyin da suka dace, cikin ruwan sanyi gami da hikima, wajen bada gudunmawarsu domin samun sauki ga ‘yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.