Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 24 sun rasa rayukansu a jihar Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba a Najeriya na cewa akalla mutane 24 sun rasa rayukansu, yayinda da wasu dama suka bace, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Tibi da Fulani a kauyen Dan Anacha.

Talla

Wata majiya daga jihar ta ce rikicin ya soma ne tun a jiya asabar, bayan da aka gano gawarwakin Fulani guda biyu da aka kasha yashe a jeji, wanda hakan yasa wasu daga ciki fara kai hari kan ‘yan kabilar Tibi da suke zargi.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar David Misal ya tabbatar da barkewar rikicin, inda ya ce an aike da jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Sai dai har zuwa lokacin da muka wallafa wannan labari hukumar 'yan sandan jihar bata sanar da alkalumman wadanda suka rasa rayukansu ba a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.