Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe babban jami’in ‘Yan Sanda a jihar Rivers

Wasu Yan bangar siyasa a Jihar Rivers dake Najeriya sun kashe Mataimakin Sufritandan 'yan Sanda Alkali Mohammed da mai tsaron sa lokacin gudanar da zaben ‘Yan Majalisun da akayi a karshen mako.

DSP Mohammed Alkali
DSP Mohammed Alkali internet
Talla

Bayanai sun nuna cewar, wasu zauna gari banza ne suka yiwa Babban jami’in kwantar bauna a Omoku da ke karamar hukumar Onelga inda suka sare kan sa.

Jihar Rivers tayi kaurin suna wajen tashin hankali lokacin zabe, kamar yadda aka gani a zaben shekarar 2015 da kuma zaben cike gurbin da ya kasa kammaluwa saboda hare-haren da suka kai ga kisan jami’in zabe da masu kada kuri’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.