ASUU ta soma yajin aiki
Kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya ta soma yajin aikin gargadi na mako guda don janyo hankalin gwamnati kan cika alkawuran da ta daukarwar kungiyar a shekara ta 2009.
Wallafawa ranar:
Shugaban kungiyar malaman, Biodun Ogunyemi ya bayyana bukatun nasu da suka hada da rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009 da 2013, wadanda suka kunshi ba da isassun kudaden tafiyar da jami’oi da biyan malamai hakkokin su da kuma daina amfani da tsarin asusun bai daya a jami’oin.
Ogunyemi yace daga yau babu koyarwa, ko jarabawa ko kuma halartar duk wani taro a daukacin jami’oin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu