Isa ga babban shafi
MDD-Najeriya

Kin taimakwa Manoma barazana ce ga tsaro inji MDD

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadi cewa kin taimakawa manoma da suka durkushe a Arewa Maso gabashin Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram, ka iya cusa musu tsatsauran ra’ayi.

Manoma na bukatar sake farfadowa a arewa maso gabashin Najeriya
Manoma na bukatar sake farfadowa a arewa maso gabashin Najeriya ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Ayyukan ta’addancin Boko Haram a jihohin Borno, Yobe da Adamawa ya durkusar da Ayyukan gona kama daga Noma hatsi, Kifi, kiwon dabobbi da kasuwanci, musamman daga shekara ta 2012 da ta’addancin ya tsananta.

Duk da sanarwa dakarun gwamnati na kwace yankunan da dama da mayakan Boko Haram ke iko da su a bara, har yanzu ana samun hare-hare ta’addanci.

A yanzu dai kungoyoyi agaji na samun hanyar kai dauki ga mutane miliyan 7, cikinsu hada wasu miliyan 3 dake fama na matsanancin rashin abinci.

Gazawa wajen sake gina tattalin arziki yankunan karkara da samar da aikin yi, ka iya jefa matasa yankunan cikin damuwa da shiga ayyukan ta’addanci, kamar yadda hukumar abinci ta Majalisar dinkin duniya ke cewa.

Majalisar tace a yanzu tana son kaiwa manoma dubu 385 dauki, domin farfado dasu da kuma samar da wadattacen abinci a yankunan da yunwa ke cigaba da yin la’anni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.