Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekau ya mayar da martani kan nadin Barnawi

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da sakon murya a yau Alhamis, inda ya tabbatar cewa, yana nan kan matsayinsa duk da kungiyar IS ta bayyana Abu Musab al-Barnawi a matsayin sabon jagoran reshenta a yammancin Afrika.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. AFP/Capture d'écran vidéo
Talla

A cikin sakon muryar na tsawon mintina 10, Shekau ya ce, ya kamata mutane su gane cewa, "muna nan amma ba za mu haifar da hatsaniya ba a bainal jama’a, kuma za mu rayu akan karantarwar Al-Kur’ani".

Shekau ya ci gaba da cewa, har yanzu suna kan akidarsu ta jama’atu Ahlisunnah Liddaawati wal Jihad yayin da ya bayyana Barnawai a matsayin kafiri.

Wani dan jaridar kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP da kuma kwararren masanin tsaro a birnin Berlin na Jamus sun gudanar da bincike, inda suka tabbatar cewa, lallai sabuwar muryar ta Shekau ce.

Shugaban na Boko Haram ya fitar da sabuwar muryar ce a matsayin martani ga rahotannin da ke cewa, an maye gurbinsa da Sheik Abu Musab al-Barnawi, tsohon mai magana da yawun kungiyar ta Boko Haram.

A jiya Talata ne wata mujallar intanet ta kungiyar IS mai fafutukar kafa daular musulunci a Iraqi da Syria ta nuna cewa, an yi hira da Barnawi da aka ayyana a matsayin sabon shugaban Boko Haram a Najeriya.

A cikin watan Maris na bara ne, Boko Haram ta yi mubaya’a ga kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.