Boko Haram ta samu makamai a sansanonin soji- Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, babu wata kwakkwarar sheda da ke nuna cewa, kungiyar Boko Haram na samun tallafin makamai daga kungiyar ISIS mai da’awar jihadi a yankin gabas ta tsakiya.
Wallafawa ranar:
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu a yayin rufe taron tattauana matsalar Bokon Haram a birnin Abuja .
Shugaban ya kara da cewa, mayakan na Boko Haram, sun samu tarin makamai ne daga sansanonin sojoji da na ‘yan sanda bayan farmakin da suka kaddamar a lokacin da suke kan ganiyar tayar da kayar baya a Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu