Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya umarci a zakulo maharan Enugu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa jami’an tsaron kasar umurnin zakulo wadanda suka kai hari kan al’ummar Ukpabi Nimbo da ke jihar Enugu a ranar Litinin domin fuskantar hukunci.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari REUTERS
Talla

Ana zargin Fulani makiyaya da kaddamar da farmakin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40.

Shugaban ya bayyana aniyarsa ta kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya a duk inda suke.

Matakin na zuwa ne bayan an zargi shugaban da kawar da kai daga hare- haren da ake zargin Fulanin da aikatawa, kuma daga cikin ma su zargin Buhari da rashin daukar mataki har da kungiyar Kiristocin Najeriya reshen arewacin kasar wato CAN.

Dangane da zargin da ake yi wa Buhari, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Minsitan matasa da wasanni Barr. Solomon Dalung.

03:34

Zargin Buhari akan hare- haren Fulani

Shi ma Ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce, gwamnatin kasar na gudanar da aiki a sirce domin kawo karshen kashe-kashen.

Ana yawan zargin Fulani makiyaya da kaddamar da farmaki a wasu wurare musamman kauyuka, abinda shugabanninsu suka musanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.