Isa ga babban shafi
Najeriya

Zakzaky na fama da shanyewar gefen jiki

Shugaban mabiya akidar Shi’a a Najeriya, Sheik Ibrahim Zakzaky na fama da matsalar shanyewar gefen jiki kuma idonsa daya ya tsiyaye saboda harbin bindiga a tarzomar da ta barke tsakanin almajiransa da sojoji kamar yadda lauyoyinsa suka sanar.

Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Talla

Tun bayan rikicin a watan Disamban bara, ake tsare da Zakzaky tare da matarsa, Zennat wadda itama ke cikin wani hali kamar yadda lauyoyin suka ce.

A karon farko kenan da aka bai wa lauyoyin damar ganawa da shi makwanni biyu da suka gabata, bayan magoya bayansa sun kagu su san hakikanin halin da jagoransu ke ciki yayin da aka yi ta rade radin cewa ya mutu.

Yanzu haka dai Zakzaky na kalubalantar matakin ci gaba da tsare shi a wata Kotu da ke birnin Abuja, inda ya bukaci a biya shi diyyar Naira bliyan biyu saboda barnar da aka yi ma sa kamar yadda lauyoyin suka tabbatar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, gwamnatin jihar Kaduna ta bakin sakatarenta Balarabe Lawal, ta bayyana cewa, an binne gawarwakin 'yan shi’a 347 a wani katafaren kabari da aka haka a makabartan garin Mando.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.