Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin kaduna ta kafa kwamitin binciken rikicin Zaria

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta kafa wani kwamitin shari’a domin binciken rikicin da ya barke tsakanin shugaban sojin kasar, Laftanar Tukur Buratai da mabiya Shi’a a garin Zaria, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari tare da Gwamnan jihar Kaduna Nasir el Rufai
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari tare da Gwamnan jihar Kaduna Nasir el Rufai vanguardngr.com
Talla

Kwamitin dai na karkashin mai shari’a Mohammed Lawal Garba, alkalin kotun daukaka kara da ke Fatakwal.

Wasu daga cikin mambobin kwamitin sun hada da Farfesa Salihu Shehu da Farfesa Umar Labdo da Malam Salihu Abubakar da Farfesa Awwalu Yadudu, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin shari’a.

Wata sanarwa da Samuel Arunwa mai magana da yawun gwamnan kaduna Nasir el-Rufai ya sanya wa hannu ta bayyana cewa za a kaddamar da kwamitin cikin mako mai zuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.