Shugaban Nigeria Na Kan Hanyar Zuwa Kasar China
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari na kan hanyar sa ta zuwa kasar China yau Lahadi a kokarin da yake yi domin maido da daraja da martaban kasar a idanun duniya.
Wallafawa ranar:
Ziyarar ana ganin bata rasa nasaba da kokarin Gwamnatin kasar na farfado da zirga-zirgan jiragen kasa da kuma samarda hasken wutan lantarki a fadin kasar.
Shugaban Nigeria zai kuma tattauna da Shugaban kasar China Xi Jinping.
A halinda ake ciki Mataimakin Shugaban kasar Yemi Osibajo ranar Asabar ya ziyarci Kano domin yin jaje ga 'yan kasuwa da suka yi hasara sakamakon gobara.
A jawabin sa Mataimakin Shugaban kasa ya ce Shugaba Buhari na sane da halin kunci da jama'a ke ciki, kuma za'a share masu hawaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu