Isa ga babban shafi
Najeriya

DSS ta Zargi Biafra da kashe mutane 55 a jahar Abia

Rundunar ‘yan sandan cikin Najeriya ta sanar da gano wani makeken kabari dauke da gawarwakin mutane 55 da aka ce masu fafutukar kafa kasar Biafra ne suka kashe su kafin daga bisani sun binne su a wani daji da ke kusa da Umuahiya a jihar Abia da ke kudancin kasar.

Zanga zangar yan kungiyar Biafra a birnin Aba na jahar Abia a Najeriya
Zanga zangar yan kungiyar Biafra a birnin Aba na jahar Abia a Najeriya AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Sanarwar hukumar ‘yan sandan ta DSS ta ce an gano kabarin a lokacin da suke bincike game da wasu ‘yan arewacin kasar biyar da aka sace, kuma bisa ga dukkanin alamu kungiyar ta ‘yan Biafara mai suna IPOB ce ta aikata kisan.

Tun watan Nuwambar shekarar 2012 aka kaddamar da jamhuriyyar Biafra tare da kafa tutarta kuma tun lokacin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ke yunkurin tada zaune tsaye da sunan neman kafa kasar Biafra ba tare da samun nasara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.