Isa ga babban shafi
Najeriya

A na binciken sace yarinya a Sokoto

Gwamnatin Sokoto ta bai wa hukumar kare hakkin dan Adam umarnin gudanar da bincike kan jita-jitar da ake yadawa na sace wata yarinya ‘yar shekaru 15 daga Benue kuma aka kawo ta Sokoto tare da yi mata auren tilas.

Patience Paul da ake zargin an sato ta daga Benue zuwa jihar Sokoto.
Patience Paul da ake zargin an sato ta daga Benue zuwa jihar Sokoto. thewhistler.ng
Talla

Gwamnan jihar ne, Aminu Tambuwal ya bayar da umarnin bayan wata kungiyar Idoma ta bukaci Sarkin musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar da shugaban ‘yan sandan Najeriya, Solomom Arase su shiga cikin lamarin.

Wannan dai na zuwa ne bayan jita- jitar da aka yi ta yadawa na cewa an sato Patience Paul daga jiharta ta asali wato Benue, sannan kuma aka boye ta a fadar sarkin musulmi da ke Sokoto.

Tambuwal ya umarci hukumar da ta gaggauta bincike tare da ba shi sakamako.

Wannan zancen na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan da rundunar 'yan sandan Najeriya ta mika wa wasu iyaye daga jihar Bayelsa 'yarsu da ake zargin sace ta aka yi sannan aka tilasta ma ta shiga musulunci a garin Kano.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.