Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai yi hira da 'yan jaridan Najeriya a yau

A yau laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tattauna da ‘yan jaridu kai tsaye ta kafafen yada labarai na kasar, inda ake sa ran zai amsa tambayoyi akan batutuwa da dama da suka shafi Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Francois Picard/France 24
Talla

A karon farko kenan tun bayan darewarsa kan karagar mulki da Buhari zai yi irin wannan tattaunawar wadda gidan talabijin na NTA da gidan rediyo na FRCN za su watsa kai tsaye da misalin karfe bakwai na dare agogon kasar.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin watsa labarai ne, Femi Adesina ya sanar da haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta ce, sauran gidajen rediyo da talabijin na kasar za su iya rabuwa da NTA da FRCN domin samun damar watsa shirin ga masu ga masu saurare da kallo.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fama da matsaloli da suka hada da na ta'addanci da tattalin arziki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.