Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC ta kama Bafarawa da Dokpesi

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Sokkoto Attahiru Bafarawa da shugaban gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi sakamon zargin su da hannu wajan yin sama da fadi da kudaden da aka ware domin siyan makamai.

Tsohon gwamnan jihar Sokkoto, Attahiru Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sokkoto, Attahiru Bafarawa Bioreports
Talla

Rahotanni sun ce an kama Bafarawa da Raymond ne a gidajensu da ke babban birnin Abuja, inda aka tasa keyarsu zuwa shalkwatan hukumar domin amsa tambayoyi a binciken da ake yi dangane da karkatar da akalar makudan kudade daga cikin Naira biliyan 643 da ya kamata a siyi makamai da su,matakin da ya jefa jami’an tsaron kasar da kuma fararen hula cikin hatsari a yakin da Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram.

Ana zargin Bafarawa da karban kudaden da yawansu ya zarce Naira biliyan 4 daga ofishin tsohon mai bai wa shugaba kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki, yayin da shi kuma Dokpesi ake zargin sa da karban sama da Naira biliyan 2 daga ofishin.

Tuni dai aka sake kama Kanar Sambo Dasuki kan wannan badakalar da kuma tsohon ministan kudi Bashir Yuguda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.