Afrika ta kudu na kan gaba a cin hanci da rashawa
Kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa a duniya ta Transparency International ta ce kasar Afirka ta kudu ta fi kowacce kasa a Afirka samun karuwar cin hanci da rashawa a cikin watanni 12 da suka wuce.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotan ya ce a karon farko ana samun mutanen da ke fitowa fili suna karar jami’an gwamnati a kasashensu da ke bukata ko karbar cin hanci da rashawa.
A cikin kasashe 18 daga cikin 28 da aka gudanar da bincike akan su a Afirka, akasarin mutanen da aka tuntuba sun bayyana cewar gwamnatocin su basa daukan matakan da suka dace domin magance matsalar.
Binciken ya nuna cewar an samu karuwar cin hanci a kasashen Saliyo da Najeriya da Liberia da kuma Ghana, yayin da aka samu raguwarsa a kasashen Botswana da Burkina Faso da Lesotho da kuma Senegal.
Kungiyar ta ce ta tuntubi mutane 43,143 a kasashe 28 kafin fitar da rahotan ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu