Najeriya
Kotun kolin Najeriya ta dakatar da shari'ar Saraki
Kotun koli ta Najeriya ta dakatar da shari’ar da kotun kula da da’ar ma’aikata ke yi wa shugaban majalisar dattawan kasar, Bukaola Saraki.
Wallafawa ranar:
Talla
Gabanin wannan matakin dai, manyan kotunan kasar sun yi watsi da karar da Saraki ya shigar musu na neman dakatar da shari’ar da ake yi masa.
Kotun kolin ta ce, a dakatar da shari’ar har nanda wani lokaci kafin ta yanke hukuncin karshe game da karar da ya shigar mata.
Ana tuhumar saraki da aikata laifuka 13 da ya hada da bayar da bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka, duk da dai ya musanta zargin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu