Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram na ci gaba da kisa- Amnesty

Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewar har yanzu kungiyar Book Haram na ci gaba da hallaka jama’a duk da nasarorin da sojin Najeriya ke samu a kansu.

Boko Haram ta hallaka mutane da dama a cikin wannan shekarar.
Boko Haram ta hallaka mutane da dama a cikin wannan shekarar. AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar ta nuna cewar, akalla mutane dubu 1 da 600 Boko Harsm ta kashe a cikin watanni hudu da suka gabata, daga cikin mutane dubu 3 da 500 da kungiyar ta kashe a cikin wannan shekarar.

Daraktan bincike na Amnsety International, Netsanet Belay ya bukaci gwamnatocin kasahsen dake fama da matsalar Boko Haram da su kara kaimi wajen kare rayukan fararen hular da kungiyar ke hallakawa.

Tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashi takobin kawo karshen kungiyar ta Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.