Matsalar sarar maciji na kokarin zama barazana ga al’ummar garin Billiri dake jihar Gombe a Arewacin Najeriya.Wannan yasa mahukunta sun aike da tawaggar kwararru daga ma’aikatar lafiyar kasar zuwa yankin, don nazari kan lamarin.Kan wannan ne Nasiruddeen Muhammad ya tattauna da Darakta a ma’aikatar lafiyar kasar, Dr. Nasiru Sani Gwarzo, da kuma ke cikin tawaggar da suka je yankin.
Sauran kashi-kashi
-
Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.02/05/202403:06 -
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23 -
Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya
Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500 a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.29/04/202403:27 -
Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa
Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya.26/04/202405:17