Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta daure Wani Dan Najeriya mai alaka da Al Qaeda

Wata kotun Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 22 akan wani Dan Najeriya mai suna Lawal Olaniyi Babafemi da aka kama da aikata laifukan ta’addanci.

Makaman Mayakan Al Qaeda
Makaman Mayakan Al Qaeda http://syrianfreepress.wordpress.com
Talla

Dan Najeriya ya amsa laifin zargin da ake masa kan yana da alaka da kungiyar Al Qaeda reshen Yemen, kuma an yanke masa hukuncin ne a wata kotun Amurka a Brooklyn.

Bayanan kotun sun ce Babafemi yana da alaka da Umar Faruk Abdulmutallab da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai akan yunkurin tarwatsa wani Jirgin Amurka a ranar Kirsimeti a 2009.

An bayyana cewa sau biyu Babafemi na tafiya Yemen daga Najeriya a 2010 da 2011 inda ya ke taimaka ma Al Qaeda a bangaren yada labarai tare da karbar kudi domin horar da wasu sabbin mayaka daga Najeriya da ke magana da harshen Ingilishi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.