Isa ga babban shafi
Najeriya-kano

'Yar kunar bakin wake ta kai harin bam a kano

'Yan sanda Jihar kano da ke Najeriya sun tabbatar da cewa wata yarinya da ta kai harin kunar bakin wake a kusa da Masallaci Aliyu bin abu Talib da ke kusa da shataletalen 'Dangi' ita kadai ta rasa ranta, sai mutum guda da ya jikata.

REUTERS/Stringer
Talla

Harin dai ya afku ne da misalin karfe 9 da 'yan mintina agoggon Najeriya, bayan kammala sallah Taraweeh a masallacin.

Wakilin RFI a kano Abubakar Isa Dandago ya rawaito cewa wani ganau ya shaida masa cewa yaga wata yarinya a lokacin da ta ke barin masallacin, kuma ya ga sassan jikinta a kasa bayan fashewar bam din.

01:17

Abubakar Isa Dandago dauke da Rahoto kan Harin kunar bakin wake a Masallacin Aliyu Bin Abi talib

Umaymah Sani Abdulmumin

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.