Isa ga babban shafi
Najeriya

Dattawan Najeriya sun nemi 'yan majasun kasar su hade kai don samar da ci gaba

A Najeriya kwamitin dattawa Kasar da ya jagoranci Sasanta ‘yan takarkarin siyasa a lokacin yaki neman zaben kasar da ya gabata, sun bukaci ‘yan majalissun kasar, dama ragowan ‘yan siyasa da su hadda kan su domin ci da kasar gaba.

Majalisar dokokin Najeriya dake Abuja
Majalisar dokokin Najeriya dake Abuja AFP
Talla

Wannan kira dai na zuwa ne, bayan dambarwar siyasar da aka samu a zauren Majalissun, a lokacin zaben sabbin shugabannin, lamarin da kwamitin ke gani cewa wanan lokaci ba na rikici ba ne.
A baya an sami rarrabuwar kanun ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, wadda kuma keda rinjaye a majalisun dattijai da na wakilai, sakamakon takun sakar da aka samu kan zaben shugabannin majalisun.
Sai dai kuma alamu na nuna cewa shugabannin jami’iyyar sun samo bakin zaren dinke wannan barakar, da wasu suka yi tunanin zata zama mata barazana a ci gaba da gudanar da ayyukan mulkin kasar.
Wasu shugabannin jam’iyyar sun yi fatan ganin an zabi Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugabana majalisar Dattijan kasar, sannan kuma a zabi Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai, amma kuma sai wasu ‘yan majalisun suka sa kafa suka yi atali da wannan bukata.
Zaben ya jefa majalisun dokokin kasar 2 cikin rudani na wani dan lokaci, amma kuma tuni ‘yan majalisun suka daidaita tsakanin junansu, don ci gaba da aiki.
Sai dai duk da haka jam’iyyar adawa ta PDP tayi riba da wannan barakar, ganin yadda ‘ya ‘yan PDP din suka sami manyan makamai na shugabancin majalisun.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.