Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Najeriya na kan hanyar shi ta zuwa taron AU a Afrika ta Kudu

Yau Asabar shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai tashi zuwa kasar Africa ta Kudu, inda zai halarci taron kungiyar hadin kan nahiyar Africa.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari twitter
Talla

Wata sanarwar da mai baiwa shugaban shawara na musamman kan harkokin yada labaru Femi Adesina ya rabawa manema labaru tace shugaba Buhari zai kuma yi amfani da wannan damar wajen ganawa da shugabanni wasu kasashen, don nemo hanyoyin bunkasa tsaro a kasar.
A karon farko kuma, Shugaban na nigeria zai jagoranci taron kwamitin tsaron kungiyar ta taraiyar Arfica.
Taron da shine karo na 25, zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tsaro a nahiyar Africa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.