Isa ga babban shafi
Ta'addanci

Hare-haren ta’addanci sun karu a duniya-bincike

Mutanen da ke mutuwa a hare haren ta’addanci ya karu da kashi 61 tsakanin 2012 zuwa 2013, kamar yadda alkalumman wani binciken ayyukan ta’addanci a duniya suka nuna. Binciken yace Mayakan IS da Al Qaeda da Boko Haram da Taliban ke da alhakin kisan Jama’a.

Wani harin bam da aka kai a birnin Kabul a Afghanistan
Wani harin bam da aka kai a birnin Kabul a Afghanistan Reuters
Talla

Alkalumman binciken sun ce an samu karuwar hare haren ta’addanci da kashi 44 a 2013 inda aka kai hare-hare kusan 10,000.

Amma rahoton binciken yace mutane 18,000 suka mutu a hare-haren ta’addanci da aka kai a 2013. Binciken yace kasar Iraqi ce ta fi fama da hare-haren ta’addanci .

Najeriya da ke fama da Boko Haram tana cikin jerin sahun kasashe biyar da aka fi kai hare haren ta’addanci bayan Iraqi da Afghanistan da Pakistan da Syria.

Sakamakon binciken yace Mayakan Al Qaeda da Taliban da Boko Haram da kuma IS suna kai hare hare ne da sunan gwagwarmayar shinfida Musulunci bisa akidar Wahabbi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.