Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Hamas ta ji dadin harin da aka kai wa Isra’ila

Kungiyar Hamas ta yaba da harin da wasu ‘Yan bindiga suka kai wa Isra’ila a wajen da Yahudawa ke ibada wanda ya kashe mutane hudu. Hamas tace martani ne ga kisan Bafalasdine direban mota da aka tsinci gawarsa a ranar Lahadi.

'Yan sandan Isra'ila sun killace inda aka kai hari a wajen Ibadar Yahudawa
'Yan sandan Isra'ila sun killace inda aka kai hari a wajen Ibadar Yahudawa REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

A cikin wata sanarwa, Kungiyar Hamas da ke iko a Gaza tace martani ta mayarwa Isra’ila a kan kisan Yusuf Ramuni.

A ranar Lahadi ne aka tsinci gawar Ramuni a cikin mota a rataye, a cikin wani yanayi da ‘Yan sandan Isra’ila suka danganta da kisan kai.

Da safiyar yau Talata ne kuma wasu ‘Yan bindiga suka kai hari a wajen ibadar Yahudawa a birnin Kudus tare da kashe mutane hudu.

‘Yan sandan Isra’ila sun yi zargin cewa Falasdinawa ne suka kai harin dauke da bindiga da gatari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.