Isa ga babban shafi
Najeriya

Heartland da Lobi Stars za su nemi lashe kofin Kalubale a Najeriya

Kungiyar Heartland da Lobi Stars a Najeriya sune za su buga wasan karshe na neman lashe kofin kalubale da za’a buga a ranar Lahadi a birnin Lagos, bayan sun samu nasarar lashe wasan kusa da karshe.

'Yan wasan Lobi Stars a lokacin da suke karawa da kungiyar Rangers
'Yan wasan Lobi Stars a lokacin da suke karawa da kungiyar Rangers Naija Football
Talla

A jiya Laraba ne Heartland ta doke Prime FC a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan kammala wasan babu ci a birnin Ilori.

A daya bangaren ma, Lobi Stars ta samu nasarar doke Kano Pillers a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan kammala lokuttan wasan babu kwallo a raga.

Lobi Stars dai ta taba lashe kofin a shekarar 2003 bayan doke kungiyar Sharks ci 2-0. Sannan kungiyar ta taba buga wasan karshe tsakaninta da Eyimba a shekarar 2005 amma Eyimba ce ta lashe kofin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.