Isa ga babban shafi
Najeriya

An Kama 'Yan Wasa Biyu Da Miyagun Kwayoyi

An sake samun wani dan Najeriya da shan miyagun kwayoyi wajen gasan wasannin motsa jiki da akeyi a New Delhi na Kasar Indiya.Na baya bayan nan shine Samuel Okon wanda yazo na shida a tseren mita 110, bayan gudun an auna fitsarin sa aka gano cewa ya sha wani kwaya mai sa kuzari mai suna methylexanemine.Shugaban Hukumar gasan Wasannin Mike Fennell yace sun tuntubi jami'an ‘yan wasan Najeriya domin jin yadda akayi wannan dan wasa ya hambuda miyagun kwayoyi wajen gasan.Jiya wata ‘yar wasan mace daga Najeriya, Osayomi Oludamola, wadda ta lashe zinari a gudun mita 100 an gano cewa saida tayi tatil da miyagun kwayoyi kafin tayi tseren.Akwai alamun wata kila a kwace lamban zinari data samu. 

Wani lebura kwance kusa da  filin wasa na Thyagraj dake New Delhi
Wani lebura kwance kusa da filin wasa na Thyagraj dake New Delhi rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.