Isa ga babban shafi
Libya

Yan tawayen Libya sun bayyana fafatawa da dakarun gwamnati a garin Brega

Bayanan dake fitowa daga kasar Libya, na nuna cewar ana ta dauki ba dadi, tsakanin Yan Tawayen kasar, da kuma dakarun shugaba Muammar Ghadafi, a Gabashin garin Brega.Wata majiya ta ce, 'yan tawayen na cigaba da kutsa kai zuwa Brega, duk da hare hare da manyan makaman da dakarun Ghadafi keyi, amma babu wata majiya ta daban da ta tabbatar da ikirarin.Kungiyar dake kula da 'yan bakin haure ta duniya, tace akalla bakin haure 625,000 yanzu haka ke cikin halin kakanikayi, sakamakon rikicin kasar Libya.Kakakin kungiyar, Jemini Pandaya, ta ce kafin barkewar rikicin kasar ta Libya, bakin haure miliyan daya da rabi zuwa miliyan biyu da rabi ne, akasari 'yan kasashen Afrika da Asia, ke aiki a Libya, kuma sun kwashe shekaru da dama a kasar.Jami’ar ta ce, yawancin wadanna mutane sun rasa inda zasu sa kansu, sakamakon tashin hankalin. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.