Isa ga babban shafi
IMF

Lagarde ta Karbi shugabancin IMF

Tsohuwar Ministan Kudin kasar Faransa, Christine Lagarde, ta fara aiki a matsayin sabuwar shugabar Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF.Ta zama mace ta farko data rike mukamun, bayan da mambobin gudanarwa 24 suka amince da zabenta.An samu gurbi bisa shugabancin hukumar ta IMF, bayan murabus da Dominique Strauss-Kahn ya y, bayan cafke shi kan zargin yunkurin fyade a birnin New York, abunda ya musanta.Lagarde Ba-Faranshiya, ta samu goyon bayan Amurka, Tarayyar Turai da kasashen China, Brazil da Indiya, abunda yasa ta doke abokin takararta Agustin Carstens dan kasar Mexico.

Christine Lagarde Sabuwar Shugaban Hukumar IMF ko FMI
Christine Lagarde Sabuwar Shugaban Hukumar IMF ko FMI Reuters/TF1
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.