Isa ga babban shafi
Faransa

Ministan Kudin Faransa Christine Lagarde zata nemi shugabancin IMF

Ministan Kudin kasar Faransa, Christine Lagarde, ta kaddamar da yunkurin ta, na takarar shugabancin Hukumar bada lamini ta duniya, IMF. Inda ta ke da goyon baya daga shugaban kasar ta Faransa Nicolas Sarkozy.Minista Lagarde ta zama ‘yar takara ta gaba gaba wajen gadon tsohon shugaban hukumar ta IMF Domiinique Strauss-Kahn, wanda ya yi murabus bisa dalilan zarginsa da yunkurin fyade. Kuma tana da goyon bayan kasashen Turai.Wannan daidai lokacin da kasashe masu tasowa ke cewa, lokaci ya wuce da za’a ce sai wanda ya fito kasashen Turai ne zai shugabanci Hukumar.Kasashen Brazil, Russia, India, China da Afrika ta kudu, sun ce cancanta ya kamata a dinga dubawa wajen nada shugaban Hukumar, ba wai inda ya fito ba.Kasashe Masu tasowa sun bayyana damuwarsu kan yadda kasahsen Turai ke cigaba da mamaye kujerar shugabancin Hukumar Bada lamini ta Duniya, inda suka bukaci kawo sauyi.Kasahsen Brazil, Russia, India, China da Afrik ata kudu, sun ce zabin shugaban Hukumar daga Turai, na dakushe kimar hukumar. 

Christine Lagarde annonçant sa candidature au FMI, à Paris, le 25 mai 2011.
Christine Lagarde annonçant sa candidature au FMI, à Paris, le 25 mai 2011. REUTERS/Jacky Naegelen
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.