Isa ga babban shafi
IMF

Tsuguni ba ta karewa Tsohon shugaban Hukumar IMF Strauss Kahn ba

BISA Dukkan alamu, tsuguni ba ta karewa Tsohon shugaban Hukumar Bada lamini ta Duniya, Dominique Strauss Kahn ba, ganin wata marubuciya, Tristane Banon, na shirin gurfanar da shi a gaban kotu, kan wani zargin yunkurin fyade.Lauyan marubuciyar David Koubbi, ya ce karar zata maida hankali ne kan wani lamari da ya auku a shekara ta 2003, lokacin da marubuciyyar taje yin hira da Dominique Strauss Kahn a wani gida dake birnin Paris.Bayanan abinda ya faru a wancan lokaci, ya biyo bayan zargin da wata ma’aikaciyar otel ta yiwa Dominique Strauss Kahn, a kasar Amurka, inda Tristane Bannon ta ce, ita ma ya kai mata irin wannan harin.Ta ce duk da yake bata shaidawa Yan Sanda ba, ta gabatar da lamarin a wani shirin gidan talabijn.Wanda take wannan zargi dai, ta ce lokacin da taje gidan nasa, ya ce ba zai hira da ita ba, sai ta rike hannunsa, da kuma taki, sai ya kama ta kokawa, inda ya nemi kwance rigar nonon ta, ya kuma zuge wandansa, amma sai Allah ya kubutar da ita.Lauyan nata, ya ce yau Talata ne ake saran gabatar da karar. Mai Magana da yawun Jam’iyar Gurguzu, Benoit Hamon, yayi watsi da duk wani yunkuri na ganin Strauss Kahn ya shiga takarar shugabancin kasar. 

Tsohon Shugaban Asusun Bada lamuni Dominique Strauss-Kahn
Tsohon Shugaban Asusun Bada lamuni Dominique Strauss-Kahn REUTERS/Allan Tannenbaum
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.