Isa ga babban shafi
Girka

Zanga Zanga Game da Matsalar Tattalin Arziki

Ma’aikatan kasar Girka sun shiga yajin aiki na sa’o’i 24 yau Alhamis, wanda ya gurgunta harkokin sufuri da harkokin yau da kullum, domin nuna rashin jin dadi akan matakan da gwamnati ta ke dauka na kawo sauye sauye.Masu zuba jari sun ci gaba da saka ido bisa lamarin da ya janyo tada kudion haraci, rage albashi da shirin rage kudaden fansho.Masu zanga zangar sun yi maci zuwa majalisar dokokin kasar da safiyar yau Alhamis, abun da ya zama zanga zanga mafi girma tun bayan ranar 5 ga watan Mayu da kimanin mutane uku suka hallaka.An rufe makarantu yayin da asibitoci ke gudanar da aiyukan jifa jifa.Wannan ya zo daidai lokacin da shugaban gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ke kirar samun dokoki tafiyar da kudade. Ta nemi kasashe su hada hanu wajen gudanar da aikin karfafa hukumomin kudaden.

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.