Isa ga babban shafi
Bangkok-Thailand

Soji Sun Kaddamar Da Sabbin Hare Hare Kan Masu Zanga Zanga

DAKARUN Kasar Thailand, sun sake kaddamar da sabbin hare hare kan masu zanga zanga yau da safe, bayan sun kutsa kai inda masu jajayen kayan sukayi sansanin.Rahotanni sun ce ana ta jin harbe harbe na tashi, a Yankunan da masu zanga zangar suke, yayin da sojin ke ta kutsa kai.Wata majiya tace, cikin mutanen da aka kashe yau, sun hada da wani Dan Jarida daga kasar Italy, da kuma masu zanga zanga biyu.Gwamnan Birnin Bangkok, Sukhumbond Paribatra, yace babu yadda za’a magance wannan tashin hankali, ba tare da zub da jinni ba, da kuma rasa wasu rayuka.Gwamnan ya kara da cewa, babu yadda Gwamnati zata gudanar da zabe a wannan lokaci, da hankula suka tashi, domin ana iya samun sabbin tashin hankula a wuraren yakin neman zabe.Tuni dai Gwamnatin kasar, tayi watsi da tayin da tayi a baya, na gudanar da zaben, da kuma bukatar tattaunawa da masu zanga zangar suka sake gabatarwa.  

REUTERS/Chaiwat Subprasom
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.