Isa ga babban shafi

Firaministan Falasdinu Shtayyeh ya sanar da murabus din gwamnatinsa

Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh, ya sanar da mika murabus din gwamnatinsa, wacce ke mulkin wasu sassan yankin Yammacin Kogin Jordan, yana mai cewa akwai bukatar samar da sababbin matakan siyasa idan aka yi la'akari da yanayin da ake ciki a Gaza.

Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh, ya sanar da mika murabus din gwamnatinsa, wacce ke mulkin wasu sassan yankin Yammacin Kogin Jordan.
Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh, ya sanar da mika murabus din gwamnatinsa, wacce ke mulkin wasu sassan yankin Yammacin Kogin Jordan. REUTERS - CLAUDIA GRECO
Talla

Firaminista Mohammad ya ce tun a ranar Talatar da ta gaba ne ya mika takardar murabus din tasa ga shugaba Mahmud Abbas, amma dai a ranar Litinin din nan ce aka amsheta a hukumance.

Shugaba Abbas dai na fuskantar matsin lamba tun bayan barkewar rikici tsakanin Hamas da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara, na rashin fitowa ya yi Allah wadan da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Yammacin Kogin Jordan.

Shugaban gwamnatin Falasdinu Mahmoud Abbas.
Shugaban gwamnatin Falasdinu Mahmoud Abbas. AP Photo/Majdi Mohammed

Murabus din gwamnatin na zuwa ne bayan da kasashen duniya ciki harda Amurka ke kiran sauya fasalin gwamnatin Falasdinu, wacce za ta kula da dukkanin yankunansu bayan kawo karshen yakin da ake gwabzawa a Gaza.

Tun a shekarar 2007 ne dai aka raba ikon yankin Falasdinu, inda Yammacin Kogin Jordan ke karkashin Mahmud Abbas ya yin da kuma yankin Gaza ke karkashin kungiyar Hamas.

A dai ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne, mayakan Hamas suka kai hari Kudancin Isra’ila da ya hallaka kusan mutane dubu daya da dari 2, lamarin da ya sanya Isra’ila maida martanin da ya hallaka kusan Falasdinawa dubu 30, yawancinsu mata da kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.