Isa ga babban shafi

An ci gaba da zaman sulhunta rikicin Isra'ila da Gaza

Wakilai daga kasashen Masar, Qatar, Amurka, Isra’ila da kuma kungiyar Hamas na ci gaba da zaman kawo karshen yakin Isra’ila da Gaza a birnin Doha na kasar Qatar.

Wani bagare na gine-ginen da harin saman Isra'ila ya rusa a yankin Rafah na Gaza.
Wani bagare na gine-ginen da harin saman Isra'ila ya rusa a yankin Rafah na Gaza. AP - Fatima Shbair
Talla

A makon da ya gabata ne Isra’ilar ta fara sakin wasu mutane 100 da ta rike tare da wasu fursunoni ‘yan kasar Falasdinu da ta rike, yayin da a wani bangaren kasashen Qatar da Masar da kuma Amurka ke fafutukar ganin cewa an sulhunta kasashen biyu.

Wannan sulhu da Amurka, da wasu kasashen Larabawa ke kokarin yi ya ba wa al’ummar yankin kwarin gwiwar cewa, za a  iya gano bakin zaren kafin watan Ramadana da ke shirin kunno kai, nan zuwa 10 ko 11 ga watan Maris.

A wani gefen kuma akwai rahoton da ke cewa daruruwan Falasdinawa ne ke tserewa daga mahallansu da ke arewaci zuwa kudancin Gaza, sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai musu, duk da yunkurin sulhunta sun da ake yi.

Sakamkon kamarin da rikicin ya yi a yankin ne kungiyoyin ba da agaji suka daina kai dauki domin taimaka wa iyalan da rikicin ya afka wa.

A halin yanzu dai, tsoro ya mamaye zukatan al’ummar Faladinun bayan Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa za ta fara kai farmaki a Rafah, inda ya na daya daga cikin manyan biranen kasar da ke dauke da kusan mutane miliyan daya da rabi, yayin da hakan ya sa mazauna yankin tserewa zuwa iyakar Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.