Isa ga babban shafi

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa a kan mutumin da ya yi wa Isra'ila leken asiri

Mahukuntan Iran sun aiwatar da hukuncin kisa a kan wani mutumin da suka same shi da laifin yi wa hukumar leken asirin Isra’ila aiki a birnin Sistan-Baluchestan a Asabar din nan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran din ya ruwaito.

Shugaban Iran Ebrahim Raïssi.
Shugaban Iran Ebrahim Raïssi. via REUTERS - WANA NEWS AGENCY
Talla

Kamfanin dillancin labaran Iran ya  ruwaito cewa mutumin yana yi wa hukumomin kasashen waje aiki, musamman ma hukumar leken asirin Isra’ila ta Mossad, inda ya  ke ba su kundaye masu kunshe da bayanan sirri.

Ba a bayyana sunan wannan mutumin ba.

Babu wani cikakken bayani a kan yadda aka kama wannan mutumin, amma kamfanin dillancin labaran Iran ya ce an yi fatali da daukaka kara da aka yi a kan hukuncin da aka yi masa.

Hukuncin kisan da aka aiwatar a gidan yarin Zahedan na yankin Sistan-Baluchestan,  na zuwa ne kwana guda bayan da ‘yan tsageran Baluch suka kai hari a kan wani ofishin ‘yan sanda, suka kashe jami’ai 11 tare da jikkata da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.