Isa ga babban shafi

'Yan sandan Iran na cikin fargaba saboda wata matsahiya

Zarge-zarge sun yi karfi kan yadda mahukuntan Iran ke kokarin tilasta wa iyalan wata matashiya mai suna Armita Gravand wadda ake zargin ta samu larurar mutuwar kwakwalwa a sakamakon dukan da jami’an tsaro suka yi mata saboda zargin yin shigar da bata dace ba yin shiru da bakin su.

Shugaban Iran Ebrahim Raïssi.
Shugaban Iran Ebrahim Raïssi. AFP - ATTA KENARE
Talla

Kafar watsa labarai ta Iran International ta ruwaito cewa gwamnatin kasar na amfani da karfin iko wajen yi wa iyalan matashiyar da ta samu wannan lallurar barazana don su dauke ta daga birnin Tehran inda ta ke kwance a asibiti zuwa ainahin kauyensu na Jafar Abad da ke yankin Kermanshah don yi mata jana’iza a sirrance idan ta mutu.

Bayanai sun nuna cewa mahukunta na wannan kokari ne don kauce wa fitar labarin, wanda zai iya tayar da mummunar zanga-zangar da ta faru bayan mutuwar Mahsa Amini, wadda jami’an tabbatar da da’a a irin suturar mata ne suka yi mata dukan da ya yi ajalin ta.

Kididdiga ta nuna cewa wannan zanga-zanga ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 300, baya ga wadanda gwamnatin da kanta ta zartas musu da hukuncin kisa saboda kama su da hannu a tayar da zanga-zangar, sai wasu daruruwa da har yanzu ke tsare a gidajen yari.

Matashiya Armita wadda daliba ce, ta gamu da jami’an tsaron da suka lakada mata duka har ta fita daga hayyacin ta a ranar 1 ga watan da muke ciki na October, nan take aka kai ta asibiti, kuma tun wannan rana ba ta farfado ba.

Gwaje-gwajen likitoci sun nuna cewa matashiyar mai shekaru 16 ta gamu da matsalar mutuwar kwakwalwa sakamakon dukan da jami’ai masu tilasta sanya hijabi suka yi mata.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Hegaw wadda itace ta fara fallasa labarin, ta ce tun lokacin da aka kaita asibiti jami’an lafiya suka tabbatar da cewa babu wata alama da ke nuna cewa matashiyar za ta rayu.

Iran International ta ce har yanzu babu wani mosti da gwamnati ta yi a bayyane, amma dai akwai alamu da ke nuna gwamnatin na shirin bi a sannu don kauce wa fushin al’ummar kasar.

Mahsa Amini ta rasa ranta ne ranar 16 ga watan Satumbar 2022, kuma tun bayan fitar labarin ne jama’a suka fusata, yayin da suka rika jerin gwanon zanga-zanga da goyon bayan wasu kasashen ketare da kungiyoyin kare hakkin dan adam.

Mahsa Amini
Mahsa Amini AP - Jose Luis Magana

A ranar 16 ga watan Satumbar da ya gabata wato ranar da aka cika shekara guda da mutuwar ta, majalisar dokokin kasar ta kara tsananta dokar tilasta wa mata sanya hijabin yadda ya dace zuwa daurin shekaru 10 a gidan yari.

Wasu daga cikin iyalanta da suka gana da manema labarai a boye, sun ce yanzu ko a gida suna tsoron ko da kiran sunanta ne, saboda suna fargabar kila jami’an tsaro sun makala wasu na’urorin sirri, kasancewar sai da jami’an tsaro suka kwashe tsahon sa’o’i suna binciken gidan da aikace-aikace a ciki kafin a basu damar shiga.

Masu zanga-zangar mutuwar Mahsa Amini.
Masu zanga-zangar mutuwar Mahsa Amini. © @Reuters

Binciken karkashin kasa da wasu kungiyoyin hakkin dan adam suka gudanar ya nuna cewa an tilasta wa iyalan matashiyar, rattaba hannu kan wasu takardu da suka haramta musu shigar da kara kan wannan batu, a kotun cikin gida ko ta kasar waje.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da majalisar dinkin duniya sun jima suna nunawa mahukuntan Iran yatsa kan zargin take hakkin dan adam da cin zarafin mata ta hanyar buya karkashin dokokin addinin musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.