Isa ga babban shafi

A yau Isra'ila da Hamas ke sa ran sako mutanen da ake tsare da su

A yau juma’a ne a ke saran Isra’ila da Hamas su mutunta alkawurran da suka dauka na sako mutanen da suke tsare da su, hanya daya tilo da zata kawo karshen yakin da ke tsakanin su.

Wani gini da jiragen yakin Isra'ila suka rusa a garin Khan Younis da ke Zirin Gaza. 17 Oktoba, 2023.
Wani gini da jiragen yakin Isra'ila suka rusa a garin Khan Younis da ke Zirin Gaza. 17 Oktoba, 2023. REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

A safiayar yau juma’a Isra’ila ta ci gaba da kai hari yankin Gaza,a daidai lokacin da kasashen Duniya suka zura ido don ganin ko za a cimma matsaya ta gari wanda hakan zai kawo karshen asarar rayuka musamman a yankin Gaza.

Yayinda wasu alkaluma ke bayyana mutuwar ‘yan jaridu 63 biyo bayan hare-hare daga Isra’ila tun bayan barkewar wannan yaki.

Kasashe da dama ne dai suka fara kwashe al’ummar su daga yankin Gaza, kasar rasha na cikin kasashen da suka fara kwashe  ‘yan kasar ta izuwa yanzu ‘yan kasar 750 suka samu komawa gida inji ministan agaji na kasar.

Kazalika kasar Turkiya ta bakin ministan lafiya Fahrettin Koca ya ce a yau juma’a za cigaba da dawo da ‘yan kasar karo na uku izuwa yanzu dfai kasar ta dawo da yan kasar ta 150.

Ana sa rai rukunin farko na fursonin Isra’ila da ya hada mata da yara 13 za a saki da misalin karfe 4 na yamma, wanda hukumar agaji ta red cross za ta raka su zuwa mashigar rafah tare da mikasu ga sojojin Isra’ila.

Haka zalika za a sako fursonini Faladinawa 39 daga Isra’ila a wani bangare na musaya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.