Isa ga babban shafi

An jinkirta batun tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas

Wani jami'in Falasdinu ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a yau Alhamis cewa, jinkirin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas, ya biyo bayan bayanan karshe dake zuwa na cewa  ko za a sako mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma hanyoyin da ya dace a yi amfani da su .

Wani mazaunin Gaza da ya samu rauni a kai
Wani mazaunin Gaza da ya samu rauni a kai AFP - MOHAMMAD AHMAD
Talla

Tsagaitawar wadda ake kyautata zaton za ta fara aiki a yau alhamis ,said ai jami’in ya jadada cewa bangarorin biyu sun yi musayar jerin sunayen wadanda za a sako.

 A daya gefen  bayanai na nuni cewa hukumomin Isra’ila sun nemi karin haske daga daga kungiyar agaji ta Red Cross  kan yadda halin da mutanen da aka yi garkuwa da sus uke ciki kafin a sako su zuwa Masar.

Yankin Gaza
Yankin Gaza REUTERS - RONEN ZVULUN

Mai shiga tsakani daga Qatar na zai sanar da lokacin da tsagaita wutar za ta fara aiki, duk da cewa  yarjejeniyar ta biyo bayan yakin da aka kwashe makonni ana gwabzawa a zirin Gaza bayan da mayakan Hamas suka kutsa kai kan iyakar Gaza a wani harin da ba a taba ganin irinsa ba. Jami’an Isra’ila sun ce kimanin mutane 1,200 aka kashe, akasarinsu fararen hula, kuma an yi garkuwa da kusan 240.

Yankin Gaza
Yankin Gaza AP - Mohammed Dahman

Hare-haren bama-bamai da Isra'ila ta kai a kasa tun daga wancan lokacin sun kashe mutane fiye da 14,000 galibi mata da kananan yara, a cewar gwamnatin Hamas da ke Zirin Gaza.

A karkashin yarjejeniyar, za a dakatar da ayyukan jin kai tare da sakin fursunonin Isra'ila 150 na farko da aka yi garkuwa da su.

Duk wadanda za a 'yantar a karkashin kashi uku zuwa daya ko dai mata ne ko kuma masu shekaru 18 zuwa kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.