Isa ga babban shafi

Isra'ila na saukaka kai kayan agaji a yankin zirin Gaza

Kanal Moshe Tetro shugaban ma'aikatar tsaron Isra'ila mai kula da ayyukan farar hula a yankin na Falasdinu ya ce Isra'ila "tana saukaka kai kayan agaji."

Khan Younès, Sud de Gaza, le 7 novembre 2023: Mohammed Hamdan a perdu 35 membres de sa famille, sur trois générations, raconte-t-il, lors d'un raid israélien sur sa maison dont il ne reste que ce canapé.
Khan Younès, Sud de Gaza, le 7 novembre 2023: Mohammed Hamdan a perdu 35 membres de sa famille, sur trois générations, raconte-t-il, lors d'un raid israélien sur sa maison dont il ne reste que ce canapé. REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Babban jami’in na Magana ne a lokacin da ake gudanar da taron jin kai kan Gaza a Paris,duk da cewa akwai tarin  matsaloli da fararen hula ke fuskanta a yankin Falasdinu a wannan  yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas.

"Mun san cewa halin da fararen hula ke ciki a zirin Gaza ba shi da sauki,kalaman Kanal Moshe Tetro.

A yau Faransa ke karbar bakuncin taron jin kai na kokarin sakin kayan agaji ga Gaza, wanda ba zai yiwu ba saboda hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke yi tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba.

Des soldats israéliens marchent dans les décombres à Gaza, après avoir annoncé que le Hamas a perdu le contrôle du nord de l'enclave, le 8 novembre 2023.
Des soldats israéliens marchent dans les décombres à Gaza, après avoir annoncé que le Hamas a perdu le contrôle du nord de l'enclave, le 8 novembre 2023. © RONEN ZVULUN / Reuters

 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a karshen watan Oktoba, ya ce wani bala'i na jin kai yana bayyana a gaban idanunmu, wanda ya kara kiran da a tsagaita bude wuta na gaggawa.

Isra'ila ta sake kai hari a zirin Gaza a yau Alhamis inda aka gwabza fadan kasa tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hamas, lamarin da ya tilastawa dubun dubatar fararen hula tserewa zuwa kudancin yankin Falasdinu da aka yiwa kawanya.

 

Conferência humanitária para a população civil da Faixa de Gaza. Palácio do Eliseu, Paris, 9 de Novembro de 2023.
Conferência humanitária para a população civil da Faixa de Gaza. Palácio do Eliseu, Paris, 9 de Novembro de 2023. AFP - LUDOVIC MARIN

 

Bayan shafe sama da wata guda ana kai hare-haren bama-bamai, fararen hula dubu dari, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, sun ci gaba da kasancewa a makale a arewacin zirin Gaza, yankin da sojojin Isra'ila ke mayar da hankali wajen kai hare-hare.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, mutane miliyan 1.5 na mazauna zirin Gaza miliyan 2.4 ne yakin ya raba da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.