Isa ga babban shafi

Dakarun Isra'ila sun kai samame ta kasa a Zirin Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi wata kwarya-kwaryar kutsawa arewacin yankin Zirin Gaza ta kasa a cikin daren Alhamis, inda har ta yi bata-kashi da mayakan Hamas da zummar sharar fage a kan shirin da take yi na shiga yankin  ta kasa.

Dakarun Isra'ila a tankin yaki.
Dakarun Isra'ila a tankin yaki. AP - Ariel Schalit
Talla

Wannan  samame da  Isra’ila ta kai cikin Zirin Gaza ta kasa na zuwa ne bayan kusan makwanni 2 da ta shafe tana lugudan wuta a kan yankin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da daidaita sama da miliyan a wannan dan karamin ziri mai yawan al’umma.

A yayin da Isra’ila ke ci gaba da ruwan wuta a yankin na Falasdinu, a Alhamis din nan jagororin kasashen Larabawa suka yi tarayya wajen rokon a tsagaita wuta don kawo karshen ukubar da fararen hula ke sha, tun bayan da Isra’ilar ta musu kawanya, biyo bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7  ga watan Oktoban.

Abinci, ruwa  da  magunguna sun fara yanke  wa mazauna wannan yankin, kuma ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya su na fuskantar matsalar rashin man fetur da za su ci gaba da ayyukan jinkai.

Ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ce mutane dubu 7 ne suka mutu sakamakon wadannan har-hare da Isra’ila ke kai wa yankin, abin daa ke nuni da cewa tun da aka fara wannan rikici tsakanin Falasdinu da Isra’ila gwamman shekaru da suka wuce, ba a taba samun adadi na mamata irin wannan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.