Kimanin Falasdinawa dubu 3 suka mutu sanadiyar hare-haren Isra'ila
Sabbin alkaluman hukumomi sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, an kashe Falasdinawa dubu 2 da 808, yayin da Isra’ila ta samu asarar rayukan mutane dubu 1 da 400 sakamakon yakin da ake gwabzawa a Gaza.
Wallafawa ranar:
Alkaluman sun kuma nuna cewa, an samu mutane dubu 3 da 500 da suka jikkata a bangaren Isra’ila, yayin da Falasdinawa dubu 10 da 859 su ma suka samu rauni a yakin na Gaza.
A can yankin Yamma ga Kogin Jordan kuwa, an samu asarar rayukan mutane akalla 57, inda kuma sama da dubu 1 da 200 suka jikkata.
Alkaluman da kafafen yada labarai da ofishin gwamnati suka tattara a Gaza, sun nuna cewa, kashi 64 cikin 100 na mamatan da harin ya rutsa da su mata ne da kananan yara.
Mayakan Hamas sun bayyana cewa, sun kaddamar sabbin hare-haren makaman roka a yankin birnin Kudus da kuma Tel Aviv a matsayin martani kan farkamakin da suka ce sojojin Isra’ila ke kai wa fararen hula.
Yanzu haka Falasdinawa sun gudanar da wata zanga-zanga a cikin unguwanni a sassan Yankin Yamma ga Kogin Jordan, suna kira da a kawo karshen hare-haren Isra’ila a zirin Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu