Isa ga babban shafi

An daure yan kasar Iran 10 saboda samunsu da hannu a hadarin jirgin Boeing na Ukraine

An yankewa wasu ma'aikatan Iran 10 hukuncin daurin shekaru daya zuwa 10 a gidan yari saboda samunsu da hannu a hadarin jirgin Boeing na Ukraine da aka harbo a kusa da Teheran a watan Janairun 2020, wanda ya lakume rayukan mutane 176.

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa nasu a wannan hadari
Wasu daga cikin mutanen da suka rasa nasu a wannan hadari ©
Talla

Mutum da ake zargi na farko, kwamandan tsarin tsaro na Tor M-1, an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari saboda ya bijire wa umarnin manyansa ta hanyar harbo jirgin, sannan an yanke wa wasu ma’aikata 9 hukuncin daurin shekaru daga daya zuwa uku a gidan yari.

Tarkaccen jirgin da aka harbo
Tarkaccen jirgin da aka harbo National Security and Defense Council of Ukraine/AFP

Majiyar ta kara da cewa, kwamandan tsarin tsaro "ya harba makamai masu linzami guda biyu kan jirgin saman da ke aiki da jirgin PS752, sabanin umarnin , ba tare da samun izini ba da kuma saba wa umarnin."

Wannan ita ce “mafi girman hukuncin, idan aka yi la’akari da irin illar da sakamakon da ya yi zai haifar  kamar dai yada sheidu suka tabbatar.

Hukumar kula da shari’a ba ta bayar da cikakken bayani kan sunayen wadanda aka yanke wa hukuncin ba, da suka hada da jami’an tsaro hudu, kwamandan sansanin tsaron sama ko kuma wani jami’in cibiyar kula da harakokin tsaro. Majiyar ta ce masu laifin na iya daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.