Isa ga babban shafi

Iran ta tabbatar da hukuncin kisa kan wani dan adawa

Mahukuntan Iran a yau Lahadi sun tabbatar da hukuncin kisa kan wani dan adawar kasar mai ruwa biyu,Iran da Sweden da ake tsare da shi tun shekarar 2020 a Iran, matakin da mai yiwuwa zai kara dagula dangantaka tsakanin Tehran da Stockholm.

Shugaban kasar Iran  Ebrahim Raisi
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi via REUTERS - WANA NEWS AGENCY
Talla

Kotun Kolin Iran ta amince da hukuncin kisa na Habib Chaab bisa laifin cin hanci da rashawa, gudanarwa da jagorancin kungiyar 'yan tawaye da tsarawa da aiwatar da ayyukan ta'addanci da dama," in ji Mizan Online, sashin Hukumar Shari'a.

 Habib Chaab mai shekaru kimanin shekaru hamsin a cewar kafofin yada labaran Iran, an gabatar da shi a matsayin shugaban kungiyar ASMLA (Arab Movement for the Liberation of Ahvaz), wanda hukumomin Iran ke daukarsa a matsayin kungiyar ta'addanci.

Ya bace ne a watan Oktoban 2020 bayan ya tafi Istanbul, kafin wata guda ya sake bayyana a gidan yari a Iran.

Bayan yanke masa hukunci tun daga watan Janairun 2022 saboda "ta'addanci" da kuma asasa "cin hanci da rashawa a duniya", a ranar 6 ga Disamba, an yanke masa hukuncin kisa.

Wasu daga cikin mutanen da kasar Iran ke tsare da su
Wasu daga cikin mutanen da kasar Iran ke tsare da su AFP - MAJID AZAD

A watan Nuwamban shekarar 2020, gidan talabijin na Iran ya watsa wani faifan bidiyo na Habib Chaab, inda ya zargi kansa da aikata wani mummunan hari da aka kai a watan Satumban shekarar 2018 a wani faretin soji a Ahvaz, babban birnin lardin Khuzestan, da kuma yana aiki da hukumar leken asirin Saudiyya.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai alkalin kasar Iran ya yanke hukuncin kisa ga wasu mutane shida da ake zargi da kasancewa kungiyar ASMLA, inda ta zarge su da bin umarnin shugabanninsu na Turai, kamar Habib Nabgan da Habib Chaab.

Tehran ta fusata da fushin kasa da kasa bayan da ta zartar da hukuncin kisa a watan Janairun da ya gabata ga wani tsohon jami'in tsaro, dan kasar Iran Alireza Akbari da aka samu da laifin leken asiri.

A watan Fabrairu ne Jamus ta kori wasu jami'an diflomasiyya biyu da ke birnin Baline saboda hukuncin kisa da aka yanke wa dan adawar Iran da Jamus Jamshid Sharmahd dan shekaru 67 da haifuwa. An zarge shi da hannu a harin da aka kai kan wani masallaci a Shiraz, a kudancin Iran, wanda ya kashe mutane 14 a watan Afrilun 2008.

Akalla masu fasfo din kasashen yamma 16 da suka hada da Faransawa shida ake tsare da su a Iran, yawancinsu ‘yan kasar biyu ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.