Biden ya ce Amurka za ta ci gaba da bibiyar lammuran Gabas ta Tsakiya
Shugaban Amurka Joe Biden ya bar kasar Saudiyya a cikin jirginsa na Air Fiorce One a yau Asabar, lamarin da ke kawo karshen ziyararsa ta farko a yankin tun da ya hau karagar mulki, inda ya shafe kwanaki 4.
Wallafawa ranar:
Kafofin yada labaran Saudiyya sun ruwaito cewa gwamnan lardin Makka, yerima Khaled-Faisal ne ya yi wa shugaba Biden rakiya zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na Jidda.
Tun da farko a Asabar din nan, shugaba Biden ya shaida wa shugabannin kasashen Larabawa cewa Amurka ba za ta ci gaba da bibiyar lammuran yankin Gabas ta Tsakiya, kuma ba za ta bari wata kasa cikin manyan kasashen duniya ta yi mata zarra a yankin ba.
Biden ya yi wannan bayanin ne a wani taron da ya yi da shugabannin kasashe 6 da ke cikin kungiyar hadin kan kasashen yankin tekun Fasha.
A ranar Juma’a, biden ya tattauna da yerima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Mohamed bin Salman, kuma a nan ne ya tabo batun kisan dan jaridan nan, Jamal Khashoggi, inda yai yi gargadin cewa a daina musguna wa masu mabanbantan ra’ayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu