Isa ga babban shafi

Iran na nazarin fara sayar da iskar gas ga kasashen Turai

Mataimakin ministan kula da albarkatun man Iran Majid Chegeni, ya ce kasar na duba yiwuwar fara sayar da iskar gas ga Turai, biyo bayan hauhawar da farashin makamashin yayi da kuma karancinsa sakamakon yakin Rasha a Ukraine.

Daya daga cikin filayen hako arzikin iskar gas mallakin kasar Iran a yankin Asalouyeh.
Daya daga cikin filayen hako arzikin iskar gas mallakin kasar Iran a yankin Asalouyeh. © REUTERS/Raheb Homavandi/TIMA
Talla

Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairu ya sa farashin mai da iskar gas tashin gwauron zabi a duniya, a yayin da yawancin kasashen Turai suka dogara da makamashin da suke saye daga Rasha.

Lamarin dai ya kara tabarbarewa a ranar Larabar da ta gabata,  lokacin da Ukraine ta ce Rasha ta dakatar da samar da iskar gas ta wata muhimmiyar hanya a gabashinta, lamarin da ya kara haifar da fargabar cewa mamayar Moscow na iya dagula matsalar karancin makamashi a Turai.

A shekarar bara, Tarayyar Turai ta sayi iskar gas din da yawansa ya kai kusan cubic mita biliyan 155, kwatankwacin kashi 45 cikin 100 na makamashin da nahiyar ke amfani da shi.

Iran dai na daga cikin kasashe mafiya arzikin iskar gas da aka tabbatar a duniya, sai dai masana’antunta sun fuskanci takunkunkuman da Amurka ta kakaba mata a shekarar 2018 lokacin da, gwamnatin tsohon shugaba Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma tsakanin kasar ta Iran da manyan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.