Isa ga babban shafi
Nukiliyar Iran

Bukatun Rasha na barazanar kawo cikas ga tattaunawar nukiliyar Iran

Bukatun da Rasha da gabatar kan rikicinta da Ukraine, a cikin mintunan karshe na tattaunawar ta da wasu manyan kasashen duniya, sun yi barazanar kawo cikas ga shirin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran a ranar Juma'a, abinda ya sanya kungiyar EU sanar da dakatar da tattaunawar.

Babban jami’in da ke kula da manufofin kasashen ketare na kungiyar tarayyar Turai EU Josep Borrell.
Babban jami’in da ke kula da manufofin kasashen ketare na kungiyar tarayyar Turai EU Josep Borrell. REUTERS - POOL
Talla

Babban jami’in da ke kula da manufofin kasashen ketare na kungiyar tarayyar Turai EU Josep Borrell ya wallafa a shafinsa na twitter cewa an dakatar da tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar ta Iran ce, saboda wasu dalilai da suka bijiro ba tare da karin bayani ba.

A karshen watan Nuwamba aka fara tattaunawar da ake yi a Vienna babban birnin kasar Austria tsakanin kasashen Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Iran da kuma Rasha inda Amurka ta tura wakilci.

A makon da ya gabata Rasha ta ce tana neman a ba ta tabbacin cewa takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa tattalin arzikinta bayan mamayewar da ta yi wa Ukraine ba zai shafi kasuwancinta da Iran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.